Mutumin da zai kashe dala miliyan daya don tono Bitcoin dinsa a wata babbar bola

Баянан Хото,

Akwai lokacin da aka kiyasta cewa kudin na Bitcoin ya kai £210m

Kusan shekara 10 da suka gabata, James Howell ya jefar da ma’adanin bayanai na komfutarsa ​​yayin da yake shara a gidansa -inda ya manta da kudin intanet na Bitcoin da ke cikinsa.

A yanzu da darajar Bitcoin ɗin nasa da ke ciki ya kai kusan fam miliyan 150, James na shirin kashe miliyoyin kudi domin haƙe wata ƙatuwar bola da nufin gano ma’adanin bayanan komfutar da ya ɓata.

Mista Howell ya ce in har ya gano ma’adanin bayanan na komfuta, zai bayar da kashi 10 na abin da zai samu don mayar da birnin zuwa cibiyar hada-hadar kudin intanet na crypto-currency.

Sai dai, mutanen yankin sun ce haƙo wurin zai jawo barazanar muhalli.

Source link

Поділіться своєю любов'ю